Type Here to Get Search Results !

Matashi ya fara tattaki da kafa daga Birnin kebbi zuwa garin Aliero biyo bayan nassarar lashe zaben Sanata da Adamu Aliero ya yi a jihar Kebbi


Wani matashi mai suna Yusuf wanda aka fi sani da kowa naka, ya fara tattaki da kafa daga garin Birnin kebbi zuwa garin Aliero a karamar hukumar Aliero a jihar Kebbi.

Yusuf ya ce ya dau alkawari ne ga Allah cewa zai yi tattaki daga garin Birnin kebbi har zuwa garin Aliero idan har Allah ya sa Sanata Adamu Aliero ya ci zaben Sanata a 2023.

Ya kuma ce duba da irin yadda janar Aminu bande ya kawo karshen matsalar mallakar fili tsakanin al'ummar Badariya da barikin soji a garin Birnin kebbi ya sa kaunarsa ya zama wajibi a gurinsa.

Matashin ya fara tattaki ne jim kadan bayan Sallar Asuba ranar Laraba 1 ga watan Maris. Majiyar mu ta tabbbatar mana da cewa Yusuf kowa naka ya riga ya wuce garin Goru kan hanyarsa ta zuwa garin Aliero.

Ku biyo mu don karin bayani...

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies