Jummaʼa, Maris 10, 2023 at 12:01 Yamma
Kotun koli ya tabbatar da Sanata Rufai Hanga a matsayin sahihin dan takarar sanatan jam’iyyar NNPP a Kano ta tsakiya a zaben ‘yan majalisun tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan Faburairu. Legit ya wallafa.
Wannan na zuwa ne a hukuncin da kotun ya yanke a zamansa da alkalai biyar nasa karkashin jagorancin mai shari’a Inyang Okoro a ranar Juma’a 10 ga watan Maris, The Nation ta ruwaito.
Kotun ya ce hukumar zabe ta INEC ta yi kuskuren rashin maye gurbin Sanata Ibrahim Shekarau da Hanga bayan da Shekarau ya yi hijira zuwa jam’iyyar PDP.
Mai shari’a Emmanuel Agim a takardar hukuncin da ya karanta wacce mai shari’a Uwani Abba-Aji ta rubuta ta yi watsi da abin da INEC ta gabatar a baya.
Kotun ya tabbatar da hukunci biyu da babban kotun tarayya da na daukaka kara da ke Abuja suka yanke na tabbatar da Hanga a matsayin dan takarar NNPP.
BY ISYAKU.COM
Rubuta ra ayin ka