Wasu mahara da ake kyautata zaton yan fashin daji ne sun kashe dan wani fasto a kauye sannan sun sace matarsa a jihar Kaduna, rahoton jaridar Vanguard.
An fada wa yan jarida a wayar tarho cewa yan fashin dajin sun kai hari garuruwan Karimbu-Kahugu a karamar hukumar Lere na jihar Kaduna a safiyar ranar Juma'a. Legit ya wallafa.
Majiyar ta ce:
"An kashe yaron wani faston Baptist. Sun kuma yi awon gaba da matarsa da wasu mutane uku."
An yi kokari domin ji ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan Kaduna amma ba a yi nasara ba, jaridar Vanguard ta rahoto.
Amma mataimakin kungiyar cigaban yankin mai suna Kahugu National Development Association, Mr Peter Mukaddas, ya ce suna zaman makokin wadanda suka rasu.
A cewarsa, yan bindigan sun tafi kai tsaye gidan faston lokacin da suka kai hari garin kuma suka aikata mummunan abin da suka yi.
A cikin kwanakin baya-baya nan, yan bindiga sun kai hare-hare ga malaman addini musamman fastoci a jihar Kaduna, Neja da wasu jihohin na yankin arewa.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI