Alhaji Abdullahi Adamu, wani fitaccen basaraken gargaji na Yaba a yankin Abaji na babban birnin tarayya Abuja ya kwanta dama. Legit ya wallafa.
Wani dangin basaraken, Shu’aibu Abdullahi ne ya tabbatar da hakan ga jaridar Daily Trust a ranar Alhamis.
A cewarsa, marigayi Etsu na Yaba ya rasu ne a hanyarsa ta zuwa sallar Magriba a cikin masarautar tasa.
A cewar Shu’aibu, sarkin ya yanki ne kawai nan take, sai fadawansa suka yi gaggawar tafiya dashi asibiti domin duba abin da ya faru.
Sai dai, an yi rashin sa’a sarkin ya yi sallama da duniya, kamar yadda majiyar ta tabbatar..
A kalamansa:
“Yana faduwa, suka dauke shi zuwa cikin mota tare da zarcewa asibiti. Amma an yi rashin sa’a ana isa asibitin, likitoci suka ce ya rasu.”
Za a yi jana'iza a ranar Juma'a
Jaridar ta tattaro cewa, an dauki gawar dattijon basaraken mai shekaru 62 zuwa masarautar Yaba domin yin jana’izarsa da misalin karfe 9 na safiyar yau Juma’a 9 ga watan Maris.
Wannan lamari dai na zuwa ne bayan rasuwar Etsu na Kwali shi ma a babban birnin tarayya Abuja, Alhaji Sha’aban Audu Nizaz, wanda ya rasu a wani asibitin kudi na Abuja a ranar 29 ga watan Disamban bara.
BY ISYAKU.COM