Kwanaki biyu gabanin zaben mambobin majalisar dokoki a jihar Edo, an damƙe mataimakin shugaban jam'iyyar APC na jihar, Jarret Tenebe. Legit ya wallafa.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa ana zargin jami'an tsaro sun kama mataimakin shugaban APC ne bisa umarnin mataimakin gwamnan Edo, Honorabul Philip Shaibu.
Rahoto ya nuna cewa an kama Mista Tenebe ne a garinsu, Ikabigbo, ƙaramar hukumar Etsako ta yamma kuma sun tafi da shi zuwa wurin da ba'a sani ba kawo yanzu.
Tenebe ya yi kaurin suna kuma fitacce ne wajen tattara wa jam'iyyar APC magoya baya da masu kaÉ—a kuri'a kuma ya kasance É—an a mutun Kwamaret Adams Oshiomhole.
A wani bidiyo da ya watsu a kwanan nan, mataimakin shugaban APC ya caccaki mataimakin gwamnan Edo kan manyan batutuwa masu sarƙaƙiya da dama.
BY ISYAKU.COM