Ɗan takarar majalisar dokokin jihar Ribas mai wakiltar mazaɓar Ahoada ta yamma karkashin inuwar Labour Party, ya shaki iskar yanci bayan an yi garkuwa da shi.
Boma Kasim-Agida, wanda ya shiga hannun 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a kofar shiga Otal dinsa, yana hanyar dawowa daga Ralin kamfen da ya gudana a Ahoada ta yamma ranar Talata. Legit ya ruwaito.
Da yake labarta abubuwan da ya gani a sansanin masu garkuwa da mutane, Kasim Agida ya ce kwana uku ya kwashe a wurin maharan da suka sace shi amma ba su ce masa komai ba.
A kalamansa da Channels tv ta rahoto, ɗan siyasan ya ce:
"Na kwashe kwanaki uku a tare da su, daga ranar Talata zuwa Jumu'a, kuma ba su ce da ni komai ba, abinda na fahimta kamar suna jiran umarni ne daga wani."
"Ba'a biya ko naira ɗaya da sunan kuɗin fansa ba, sun ɗaure mun ido kana suka tafi da ni suka aje ni a wani wuri kusa da titin Amasoma da ke jihar Bayelsa."
Da yake karin haske kan lamarin, ɗan takarar majalisar na LP ya nuna yaƙinin cewa ɗage zabe da mako ɗaya da aka yi ya taimaka matuka gaya wajen kubutarsa daga hannun masu garkuwa
BY ISYAKU.COM
Rubuta ra ayin ka