Type Here to Get Search Results !

Allah Mai Iko: Wata Ma'aikaciyar Lafiya Ta Rasu Tana Cikin Aiki a Yanayi Mai Ban Mamaki a Zamfara


Asmau Lawali Bungudu, Ma'aikacuyar jinya watau Nurse a Asibitin Ahmed Sani Yariman Bakura da ke Gusau, jihar Zamfara ta riga mu gidan gaskiya.

Tribune Online ta rahoto cewa Asmau ta rasu ne bayan ta yanke jiki ta faɗi yayin da take tsaka da aikinta a Asibitin.

Bayanai sun nuna cewa Marigayya Asma'u ta fito wurin aiki lafiya kalau da safiyar Laraba, amma awanni bayan fara aikin ranar aka tabbatar da rai ya yi halinsa.

Kakakin Asibitin, Auwal Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce Asma'u na cikin aikinta kuma ta gwada hawan jinin kusan majinyata 30 kafin daga bisani ta faɗa wa Likita tana jin ba daɗi a zuciyarta.

A cewarsa, nan take bayan ta gaya wa Likita haka, ba zato aka ga ta yanke jiki ta faɗi, Likitoci sun yi iya bakin kokarinsu domin su ceto rayuwarta amma nan take ta rasu.

"Kwararrun Likitoci sun yi kokarin ceto rayuwarta amma nan take rai ya yi halinsa," inji PRO

Auwal Usman ya kara da shugabannin Asibitin karkashin jagorancin Dakta Usman Muhammad Shanawa, sun miƙa gawar mamaciyar hannun 'yan uwanta.

Wani ɗan gidansu marigayya Asma'u ya tabbatar da cewa ta bar gida lami lafiya da safe, ta tafi Asibitin da take aiki a matsayin ma'aikaciyar jinya.

"Za'a mata Sallah jana'iza yau da misalin karfe 5:00 na yamma a kofar gidan Malam Abdurrahman da ke Magama a garin Bungudu."

Mallam Ibrahim Isa ya rasu ne a Asibitin cikin garin Kaduna da safiyar ranar Laraba 15 ga watan Maris, 2023.

A wata sanarwa da kwamifin masallacin ya fitar, ya ce za'a yi wa mamacin jana'iza bayan Sallar Azuhur.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies