Type Here to Get Search Results !

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar NNPP Ta Fara Lashe Kujerun 'Yan Majalisar Dokoki a Kano


Wasu masu kada kuri’u a jihar Neja sun ce, wasu ‘yan siyasa sun nemi su nuna katunan zabensu sannan su rantse za su zabi ‘yan takarar da suke so kafin ba su kayan amfanin gida. Legit ya wallafa.

Daga cikin kayayyakin da aka ce za a basu akwai bokitai, taliya, kayan sakawa da Maggi, kuma hakan ba sabon abu bane a siyasar Najeriya.

Daily Trust ta tattaro cewa, ‘yan siyasa a Najeriya na amfani da kayayyakin aikin gida, sutura da kayan abinci wajen sayen kuri’un al’ummar Minna a Neja da sauran garuruwa.

Wasu masu kada kuri’un sun shaidawa jaridar cewa, an nemi su nuna katin zabe sannan su rantse da Allah za su zabi wasu ‘yan takara domin samun kayan duniya.

A yankin Tunga na Minna a jihar, wata daga cikin wadanda suka ci gajiyar wannan rabon kayan abinci, Mrs Jamila Muhammad ta ce, ta samu takiyar girkawa.

A cewarta:

“Yadi daya ake ba mutum daya na kayan sakawa. Meye mutum zai yi da yadi daya na kaya? Ba zai isa ko da karamin yaro bane.

“Na karbi taliya, amma duk da haka sai da muka yi fada da mutane saboda mun yi yawa. Idan kaga yadda mata ke kokuwa kan taliya, abin da ban mamaki.”

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies