Adamawa: Jami’an tsaro sun yi wa gidan da ake zargin ana tafka magudi a ciki kawanya


Jami'an tsaro sun yi wa wani kawanya a unguwar Dougrei da ke cikin birnin Yolan Jihar Adamawa, bisa zargin dangwala kuri'a da kuma kirkirar sakamakon zabe na bogi. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Jam'iyyar APC ce dai ta yi korafi a kan gidan, inda ta zargi ’yan PDP da kokarin tafka magudi a ciki.

Wakilinmu ya ce gamayyar jami'an tsaro na sojoji da 'yan sanda ne suka mamaye gidan sannan suka hana kowa shiga yayin da ake ci gaba da bincike kan zargin magudin a zaben da aka yi ranar Asabar.

Ya ce an ga ’yar takarar Gwamna ta jam'iyyar APC, Aishatu Dahiru Binani a kusa da gidan, yayin da magoya bayanta suka mamaye shi, kafin daga bisani ta bukaci su bar wajen.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Kwamitin Yakin Neman Zaben Binanin, Martins Yanatham Dickson, sun nuna damuwa kan yadda suka yi zargin ana kokarin tafka magudi a gidan.

Daga Kabir Anwar, Yola da Sani Ibrahim Paki


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN