APC Ta Sha Kaye A Gidan Gwamnatin Kaduna


Jam’iyyar APC mai mulkin jihar Kaduna ta sha kaye a akwatunan zaɓe biyun da ke Gidan Sir Kashim Ibrahim, fadar gwamnatin jihar. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Ɗan takarar gwamna na PDP, Alhaji Isa Ashiru Kudan ne ya lashe akwati mai lamba 014 da ƙuri’u 77 yayinda ɗan takarar APC, Sanata Uba Sani ya samu ƙuri’u 40.

Jami’in zaɓe Mohammed Baso ya ce jam’iyyun PRP da NNPP sun samu ƙuri’u ɗai-ɗaya.

Haka ma akwatu mai lamba 013 PDP ta yi nasara da ƙuri’u 69 yayinda APC ta samu 64.

Jami’in zaɓe Kalu Kelechi Michael ya ce jam’iyyar LP ta samu takwas, yayinda PRP da NNPP suka samu ɗai-ɗaya.

1 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN