Yanzu-yanzu: Bayan shan kaye a zaben sanata, fitaccen gwamnan PDP ya ba da umarnin karin girma ga ma’aikatan gwamnati

Farin ciki a Abia yayin da Ikpeazu ya sanar da karin girma ga ma'aikatan gwamnati


Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia ya ba da umarnin a gaggauta karin girma ga daukacin ma’aikata a matakai daban-daban domin kara yawan aiki kwanaki kafin zaben gwamna na 2023. Legit ya wallafa.

 A ranar Laraba, 8 ga watan Maris, gwamnan ya bayar da wannan umarni yayin wata tattaunawa da kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya, NULGE, a Ochendo International Conference Centre dake Umahia.

Ikpeazu ya bayyana cewa gwamnatin sa ta dauki ma’aikata sama da 5000 aiki duk da shawarar da wasu mutane suka bayar na a sallami ma’aikata.

Gwamnan ya kara da cewa ya fahimci abin da ke tattare da korar ma’aikata, don haka ya yanke shawarar daukar karin ma’aikata, kamar yadda rahoton jaridar Vanguard ta tabbatar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN