Type Here to Get Search Results !

Ta faru: Saurayi ya yi wa Safeto da sajen na yan sanda duka, duba abin da ya biyo baya


Wani matashi dan shekara 19, Uwanu Emmanuel, a ranar Laraba, ya gurfana a gaban wata kotun majistare ta Ado-Ekiti bisa zarginsa da cin zarafin jami’an ‘yan sanda
.

Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya rahoto. Emmanuel, wanda ba a ba da adireshinsa ba, yana fuskantar tuhuma biyu na aikata laifuka.

 Dan sanda mai shigar da kara, Insp Akinwale Oriyomi, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara da sauran jama’a sun aikata laifin ne da misalin karfe 8:30 na safe a Ado-Ekiti.

 Oriyomi ya yi zargin cewa wadanda ake tuhumar sun afkawa wani Insp Adepoju Adewunmi tare da raunata shi.

 “Wanda ake tuhumar da kuma wani mutum sun yiwa Sgt.  Duduyegbe Olatunbosun duka, yayin da yake gudanar da aikin sa na halal,” inji shi.

 A cewarsa, laifukan sun ci karo da sashe na 186 da 187(a) na dokokin laifuka na jihar EKiti 2021.

 Sai dai wanda ake tuhumar ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

 Alkalin kotun, Mista Bankole Oluwasanmi, ya bayar da belin wanda ake kara a kan kudi N50,000 tare da mutum daya da zai tsaya masa.

 Ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 26 ga watan Afrilu.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies