An tsinci gawar yaro dan shekara 4 tare da cire masa idanu, harshe da al’aura a Abuja


An tsinci gawar wani yaro dan shekara hudu mai suna Eleazar Ishiya da aka bayyana bacewarsa. An gan gawar a cikin wani rami da ke unguwar Jabi a Abuja, an cire masa harshe da al’aura da idonsa.

 Majiyoyi daga danginsa wadanda suka zanta da DailyTrust sun ce an sanar da cewa marigayi Eleazar ya bace a ranar Juma’a, 3 ga Maris, a Filin Ball, Jabi Daki Biyu, kuma an gano gawarsa bayan kwana uku.

 Wani ganau mai suna Joel Joseph, wanda yana cikin mutanen da suka tsinci gawar Eleazar a cikin ramin ya ce;

 “Lokacin da muka ga gawarsa a cikin ramin, kakarsa ta yi yunkurin shiga ciki amma na rike ta na kore ta.  Na shiga cikin ramin inda na tarar da gawar ta riga ta rube.  Harshensa da duburarsa da al'aurarsa an sare shi yayin da kuma aka kwakwale idanunsa . 

A bayyane yake cewa wadanda suka kashe shi matsafa ne kuma watakila sun jefa shi cikin rami da dare.''

Mahaifiyarsa, Precious Ishaya, ta bayyana shi a matsayin "mai wayo" dalibi ne na reno kuma shine kwaya daya tilo a gidan.

 “A ranar Juma’ar nan mai ban mamaki, Eleazar  ya dauki kudi naira 10 ya siyo alawa a wani shagon cikin unguwa sai ya bata.  Ban damu da mutuwarsa ba, sai dai yadda aka azabtar da shi har ya mutu.  

Na dangana lamarina ga Allah.  Ban san wadanda suka aikata laifin ba.  Jinin yaron zai iya shiga cikin wadanda suka kashe shi marar zuciya saboda ba shi da laifi.  

Su dauki kansu a matsayin matattu.  Na kasa yin ƙarfin hali don ganin gaɓataccen jikinsa;  daga baya ne na yi nasarar ganin gawarsa a hotuna.’’.

 Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ba ta ce uffan ba kan lamarin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN