Rundunar Ƴansandan jihar Kano ta ce, ta gano shirin wasu Ƴansiyasa na shigo da ƴandaba jihar don tada hargitsi a lokacin zaɓe. Freedom radio Nigeria ta wallafa.
Rundunar ta gargaɗi ƴan siyasar da su dakatar da wannan yunƙuri domin gudun faɗa wa hannunta.
Ƴansandan sun ce, duk wanda aka samu da hannu a tarzoma zai ɗanɗana kuɗarsa.
Rundunar ta kuma nemi jama'a da su gaggauta sanar da jami'anta duk inda suka ga baƙin fuska.
Ku tara a shirin Mu Leƙa Mu Gano da ƙarfe 7 don jin cikakken labarin.
BY ISYAKU.COM
Rubuta ra ayin ka