INEC ta ce ma’aikatan da ta samu da sakaci a zabe da ya gabata babu su a zaben gwamna


Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta dakatar da dukkan ma’aikatan da aka samu da sakaci lokacin zaben Shugaban Kasa da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata, 25 ga watan Fabirairu. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

INEC ta ce dukkansu ba za su yi aikin zaben da za a yi ba na ’yan majalisar jiha da na gwamnonin a kasar da za a yi a ranar 11 ga watan Maris.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da Kwamishinonin Zabe a ranar Asabar a Abuja.

“Yayin da muke tunkarar zaben gwamna da na ’yan majalisar jiha, dole mu kara kokari domin shawo kan matsalolin da muka fuskanta a zaben da ya gabata.

“’Yan Najeriya ba za su yarda da wani abu ba bayan wannan.

“Dukkan ma’aikacin da aka samu da sakaci, ma’aikacin INEC ne ko kuma na wucin gadi ne, ciki harda masu tattara sakamako da turawan zabe, to ba za mu kyale su yi aikin zaben mai zuwa ba.

“Dole Kwamishinonin Zabe su dauki matakan da suka dace a wuraren da aka samu hujjojin cewa an yi abubuwa ba daidai ba,” in ji Farfesa Mahmood

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN