Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kona babbar kotun jihar da ke unguwar Owutu Edda da ke karamar hukumar Afikpo ta Kudu a jihar Ebonyi.
Intelregion ta rahoto harin wanda ya faru a daren Talata, 21 ga Maris, 2023, shi ne na farko da aka kai a duk wani cibiyoyi na jama'a a jihar Ebonyi tun bayan kammala zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya na 2023.
Oluchi Uduma, magatakardar kotun ta tabbatar wa manema labarai harin a Owutu-Edda a safiyar Laraba.
A cewar ta, ‘yan bindigar sun mamaye kotun ne a ranar Talata, inda suka cinnawa ginin wuta.
Bugu da kari, Uduma ta bayyana cewa ginin kotun, takardu, da sauran kayayyaki masu daraja sun kone gaba daya.
Shima shugaban karamar hukumar Afikpo ta kudu (LGA) Chima Nkama ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce an yi wa ‘yan sanda bayani.
Hakazalika, jami’in hulda da jama’a (PRO) na rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi, Onome Onovwakpoyeya, ya tabbatar da faruwar harin.
BY ISYAKU.COM