Yadda 'yan bindiga suka binne matar sarkn Fulani a Arewa bayan karbar kudin fansa


Yan bindiga sun shaidawa iyalan sarkin Fulani na Rugan Ardo a yankin Janjala na karamar hukumar Kagarko a Kaduna cewa, sun kashe tare da binne matar shugaban kauyen, Abubakar Ardo da suka sace. Legit ya wallafa.

Hakazalika, sun bukaci iyalan nasa da su yi mata addu’ar rahama tunda ita kam sun shilla ta kiyama, inji rahoton Daily Trust.

Wakili Usman, wani dangin Ardo ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da jaridar a ranar Talata, inda yace tsagerun sun shaidawa ahalin haka ne a lokacin da suka bukaci a ba su gawarta.

A cewarsa, dangin sun roki ‘yan bindigan da su taimaka su ba da gawar matar, amma suka ji batu mara dadi daga bakin shugaban ‘yan ta’a’ddan cewa sun ma binne ta tuntuni a dajin da suke boye.

Yadda lamarin ya faru
Madakin Janjala, Samaila Babangida ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace:

“Bana nan tafi Jere sai aka kira ni cewa ‘yan bindigan sun kira sun ce tuni sun binne matar Ardo a maboyarsu. Abin da muka yi kawai shine yi mata sallah a nan.”
Ya kuma shaida cewa, da yawan mutanen Janjala, musamman mata da yara sun kaura daga yankin saboda yadda ‘yan ta’adda suka addabi kowa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN