A cewar sanarwar da Tunde Rahman na ofishin zababben shugaban kasa ya fitar, tafiyar za ta baiwa Tinubu damar hutawa da tsara shirin mika mulki gabanin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.
Rahman ya kara da cewa, zababben shugaban kasar zai tafi kasar Saudiyya daga nahiyar Turai domin yin Umrah da azumin Ramadan.
Sanarwar ta kara da cewa, “Zababben shugaban kasar ya bar filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Ikeja, zuwa Turai a daren ranar Talata.
Zababben shugaban kasar ya yanke shawarar ya huta ne bayan kammala yakin neman zabe domin ya huta a Paris da Landan, domin shirye-shiryen zuwa Saudiyya aikin Umrah (Karamin Hajji) da kuma azumin watan Ramadan da zai fara ranar Alhamis.
"Yayin da zai tafi, zababben shugaban kuma zai yi amfani da damar wajen tsara shirin karbar mulki."
“Ana sa ran zai dawo kasar nan ba da jimawa ba.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI