Yan bindiga sun kutsa cikin Fada sun yi awon gaba da iyalan Basarake a jihar Arewa


Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun yi awon gaba da mata biyu a ɗan Basaraken garin Sarkin Kudu da ke jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya auku ne ranar Jumu'a da daddare lokacin da maharan suka kutsa kai cikin fadar Sarkin da ke ƙaramar hukumar Ibbi.

Bayanai sun nuna cewa basaraken mai suna, Dansalama Adamu, ya yi tafiya ya bar yankin masarautarsa lokacin da 'yan bindigan suka shiga suka sace iyalansa. Legit ya wallafa.

Har zuwa yanzun da muke haɗa wannan rahoton, babu wanda ya san inda maharan suka yi da matan biyu da ɗan Basaraken ba kuma ba su tuntuɓi ko mutum ɗaya daga cikin iyalansa ba

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Bugu da ƙari, kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa jami'ai sun damƙe wasu da ake zargin suna da hannu a garkuwa da iyalan Basaraken.

DSP Abdullahi ya ƙara da cewa a halin yanzun dakaru sun matsa kaimi wajen ganin sun kubutar da iyalan basaraken cikin ƙoshin lafiya.

Ya ce waɗanda aka kama da zargin hannu a lamarin sun yi bayani masu matuƙar muhimmanci da zai taimakawa yan sanda wajen ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Wani da abun ya faru a kan idonsa ya ce lamarin ya faru ne a garin Agbani kuma da zuwan maharan suka bude wa motar da yake ciki wuta.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN