Jihohin PDP 7 cin 8 sun jaye kara da suka shigar kan zaben Tinubu a Kotun koli


Jihohi bakwai cikin takwas da suka shigar da kara a gaban kotun koli na neman a soke nasarar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu na jam’iyyar APC ya samu, sun janye karar da suka shigar. Intelregion ya ruwaito
.

 Sun janye karar ne a ranar Juma’a, 3 ga Maris, 2023, kuma sun shigar da sanarwar dakatar da karar.

 Jihohin sun hada da jihar Adamawa, Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Edo, Taraba da kuma Sokoto sun dauki matakin ne ta hannun tawagar lauyoyinsu karkashin jagorancin Cif Mike Ozekhome (SAN).

Sanarwar, mai kwanan wata 3 ga Maris ta ce: "Ku lura cewa masu gabatar da kara sun jaye wannan karar gaba daya a kan wanda ake kara."

 Sai dai babu wani dalili da masu shigar da kara suka bayar na yanke shawarar dakatar da karar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN