Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya alaƙanta dalilin faɗuwar sa zaɓe da ƙarar da suka shigar da Gwamnatin tarayya akan sauya fasalin kuɗi da Babban Bankin Najeriya CBN yayi. Legit ya ruwaito.
Gwamnan ya zargi cewar, wasu fulogai a cikin gwamnatin tarayya da yin yaƙi dashi tuƙuru domin ganin bai sake komawa gwamnan jihar ta Zamfara ba.
Idan za'a iya tunawa dai, Matawalle yayi takara ne a jam'iyyar APC mai mulki, inda Dauda Lawal na jam'iyyar PDP ta kayar dashi.
Bugu da ƙari, gwamna Nasir El Rufai na Kaduna, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje sun kai ƙarar Gwamnatin Tarayya zuwa Kotun ƙoli.
Abisa yunƙurin canja fasalin kuɗi tare da taƙaita anfani dasu wanda CBN ke aiwatar wa.
Matawalle yace:
"Ance tunda munje Kotu akan canja fasalin kuÉ—i na Naira. To dani, da Ganduje da El-Rufai duk sai an hukunta mu."
To amma daga wani tsagin, za'a iya tunawa Uba Sani na jam'iyyar APC da El-Rufai yake marawa baya yasha daƙyar.
Yayin da É—an takarar da Ganduje ke marawa baya, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna yasha kayi a hannun É—an takarar jam'iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf.
Matawalle yace, yadda aka cika akwati-akwati da sojoji, hakan na nufin zargin sa daidai ne, domin yace anyi haka ne don a musgunawa masu kaÉ—a kuri'a shi kuma ya faÉ—i.
A rahoton jaridar Vanguard anjiyo Matawalle yana karkarewa da:
"Kwana uku zuwa zaɓen gwamnan, sai aka turo sojoji mota 300, zuwa Zamfara.
"Adadin sojojin, da ace zasu turo mana su a yaƙi rashin tsaro, da abin ya bada citta. Amma sai suka turo mana su lokacin zaɓe"
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI