Kaico: Daga sukar gwamnan APC a WhatsApp, basarake ya kare a hannun 'yan sanda


Yan sanda sun kame basaraken Umucheke a yankin Umuobom na karamar hukumar Ideato a jihar Imo, Eze Ekene Obinali. Legit Hausa ya wallafa.

‘Yan sandan sun kama basaraken ne bayan da aka zargi ya yada wani rubutu a kafar WhatsApp da ke sukar gwamnan jihar ta Imo, Hope Uzodinma.

An ruwaito cewa, a ranar 20 ga watan Maris ne basaraken ya yada wani rubutu a shafin WhatsApp na Ideato Voice mai kama da sukar gwamnan.

Abin da ya faru aka kama basaraken
Da yake tabbatar da kamun, mai kula da shafin, Vitus Ezenwa ya shaidawa jaridar Punch cewa, an kama basaraken ne a ranar Larabar da ta gabata.

Ezenma ya shaida cewa, shi da kansa an kama shi da farko, amma aka sako shi daga bisani aka kamo basaraken.

Ya shaida cewa, rubutun da ya basaraken ya yi a halin yanzu yana hannun ‘yan sandan da suka kwamushe shi kan bayyana wata badakalar gwamnan.

Menene ke cikin rubutun?

A cewar rahoto, rubutun ya yi tsokaci kan batun da ya shafi tasirin marigayi Ahmad Gulak a zaben fidda gwanin gwamnan APC a jihar ta Imo.

Da Ezenwa yake bayani ya ce:

“Sunana Nze Dr Vitus Ezenwa. Ni ne mawallafin jaridar Ideato Voice. Ku ambace ni idan kuka ga dama. Ni shaida ne game da wannan.

“’Yan sanda sun kama ni game da rubutun saboda nine mai kula da shafin da aka yada shi, shafin Ideato Voice. An tsare ni har sai da aka kama basaraken da har yanzu yana tsare.

“Yanzu haka yana hannun sashen yaki da masu garkuwa da mutane. Tiger Base. An yi rubutun ne a ranar 20 ga watan Maris.

“‘Yan sandan sun ba da beli na ne bayan kama basaraken. An ce dole na ke zuwa ofishin ‘yan sanda kullum don ba da rahoton kai na.”

'Yan sanda sun tabbatar da kamun

A lokacin da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Henry Okoye a tabbatar da kama basaraken. Sai dai, ya ce ana ci gaba da bincike kan lamarin.

Ba wannan ne karon farko da ake kama basarake ba a Najeriya, hakan ya sha faruwa a wurare daban-daban a kasar.

A Zaria, an taba kame wani basarake bisa zargin yin lalata da wani yaro karami da ya yaudara yake zuwa wurinsa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN