Ganduje: Abba Gida-Gida ka daina riga malam masallaci


Gwamnatin Kano ta yi kira ga zababben gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi hakuri, ya daina fitar da sanarwar hukuma da sunan shawara ga jama’a.

A cewarta, irin wannan shawara za ta iya haddasa rudani na babu gaira babu dalili a cikin jihar. Jaridar Aminiya ta rahoto.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Muhammad Garba ya fitar don maida martani ga ofishin zababben gwamnan a kan su guji janye daga filayen gwamnati.

Gwamnatin Kano ta ce abin da zababben gwamnan ya yi na bayar da umarni a kan wani batu da ya shafi manufar gwamnati, daidai lokacin da gwamna mai ci har yanzu yake kan mulki, tamkar riga malam masallaci ne.

Ta kara da cewa kamar yadda yake kunshe a cikin tsarin mulkin Najeriya, Dokta Abdullahi Umar Ganduje zai ci gaba da zama gwamna mai cikakken iko har zuwa ranar 29 ga watan Mayu, kuma yana da damar gudanar da ayyukansa hatta a ranar jajiberen saukarsa daga mulki.

A Alhamis din da ta gabata ne, gwamnan mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf ya fitar da wata sanarwa wadda ya bayyana a matsayin shawara, yana kira ga masu gine-gine a filaye da wuraren gwamnati, ciki har da masallatai da makabartu da makarantu da sauransu, su dakata.

Lamarin da ya janyo zazzafar muhawara da ka-ce-na-ce musamman a shafukan sada zumunta.

1 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. Gaskiyane yakamata ya boye ra ayinsa saiya dale karagar kafin ya. Bayyana

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN