Yadda aka farke cikin mai juna biyu aka sace dan tayin da ke cikin


Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun kashe wata mai ma juna biyu, suka farke cikinta sannan suka dauke dan tayin da ke ciki. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Rahotanni sun ce an tsinci gawar matar mai juna biyu ne a yashe a kan wani juji a Rukunin Gidajen Alkalai da ke Makurdi, babban birnin Jihar Binuwai.

Aminiya ta gano cewa tsinci gawar mai juna biyun ce kwana kadan bayan ’yan sanda sun tsinci gawar wata dalibar jami’a a unguwar.

Wani ganau da ya ce a boye sunansa ya bayyana cewa mai juna biyun da aka tsinci gawarta an farke cikinta an tafi da dan tayinta, wata mai tabin hankali ce da ke yawo a yankin.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Binuwai, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa an dauke gawar zuwa mutuwari.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN