Type Here to Get Search Results !

Kotu ta sa Murja Hukunci: Kunya da abokanta sharar asibiti da masallaci


Kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Filin Hokey ta yanke jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya da abokanta hukuncin sharar masallaci da kuma asibiti. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Abokan Murja maza, wadanda aka gurfanar da su tare da ita, Idris Mai Wushirya, Aminu BBC da kuma Sadiq Shehu Shariff za su zai rika sharar Masallaci Murtala, ita kuma za ta rika share Asibitin Murtala da ke Kano.

Kotun ta yanke musu hukuncin ne a shari’ar da aka gurfanar da su kan zargin yada bata a kafar TikTok da kuma bata tarbiyya, zargin da suka musanta.

Gabanin zaman kotun na ranar Alhamis, sai da ta tura su zaman wakafi a gidan yari kan zargin.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies