Tsohon gwamnan jihar Arewa ya shiga jerin masu neman kujerar shugaban majalisar dattawa


Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana aniyarsa ta zama shugaban majalisar dattawa ta Najeriya. Legit Hausa ya wallafa.

Yari bayyana hakan ne tare da bayyana hujjar cewa, yankin Arewa maso Yamma ne ya fi ba dan takarar shugaban kasa na APC kuri’u mafi a zaben shugaban kasa na bana.

Idan baku manta ba, Bola Ahmad Tinubu ne ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Faburairu, inda ya samu jumillar kuri’u 2,652,235 daga Arewa maso Yamma.

Yari dai sanata ne dai zai wakilci Zamfara ta Yamma a majalisar dattawa ta 10 na tsawon shekaru hudu kafin a sake zabe a 2027.

Hujjojin da Yari ya bayyana
A wani bidiyon da Imran Muhammad ya yada a Twitter, an ji jigon na APC kuma tsohon gwamnan Zamfara na cewa:

“Zabe ya zo, ya tafi kuma dai shiyyar (Arewa maso Yamma)ta yi abin da ta saba na jan ragamar kawo kuri’u ga zababben shugaban kasarnmu da jam’iyyarmu.

“Duk da dai wasu mutane sun so kawo tsaiko ga hakan, amma mun yi iyakar duk kuwa da kalubalen da aka samu.

“Yanzu, muna da shugaban kasa (Tinubu) daga Kudu maso Yamma, muna da mataimakin shugaban kasa daga Arewa maso Gabas sannan Arewa maso Yamma na jira.

“Na yi imanin idan shiyya ta za ta yanke shawarin goyon bayana ba za su goyi bayan wanda bai dace ba. Na yi imanin sun san kokari na tun daga matakin shugaban jam’iyya, dan majalisa har zuwa gwamna.”

Yari dai zai gwabza ne da jiga-jigan ‘yan siyasa a Najeriya da ke neman wannan kujera ta shugaban majalisa irinsu Jibrin Barau, David Umahi, Orji Kalu, Ali Ndume da Godswill Akpabio.

An kuma kama tsohon gwamnan na Zamfara bisa zarginsa da hannu a badakalar Ahmed Idris, korarren akanta-janar na Najeriya.

An sha kai ruwa rana da ‘yan siyasan Najeriya kan badakalar kudade da kuma sace kadarar kasa tare da zuba wa a lalitarsu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN