Type Here to Get Search Results !

Karin Bayani: Tashin Hankali Yayin da Aka Tsinci Gawar Ɗan Takarar Gwamna a Gidansa


Rahotanni sun nuna cewa an tsinci gawar ɗan takarar da ke neman tikitin takarar gwamna a inuwar Labour Party a zaben fidda gwanin da ke tafe a jihar Imo, Chief Humphrey Anumudu. Legit Hausa ya wallafa.

Tribune Online ta rahoto cewa ɗan takarar ya mutu ne a gidansa da ke jihar Legas, bayan ya dawo daga taron LP wanda ya gudana a Hedkwatar jam'iyya ta ƙasa da ke Abuja ranar Jumu'a.

Jihar Imo na ɗaya daga cikin jihohin da INEC ke gudanar da zaben gwamna a lokaci daban da babban zaɓe kuma a yanzu, jam'iyyu sun fara shirin tsaida yan takara.

Me ya yi ajalin ɗan siyasan?

Jigon siyasan, haifaffen yankin masarautar Mbieri, ƙaramar hukumar Mbaitoli a jihar Imo, Anumudu, bayanai sun nuna an tsinci gawarsa a gida a yanayin da iyalansa suka kira da, "Farmakin ruhi."

A matsayinsa na Biliyoniyan ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa, ya jima yana neman takarar zama gwamnan jihar Imo da ke arewa maso gabashin Najeriya, tun 1998.

An ce shi ne halastaccen wanda ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP a shekarar 1998 kafin daga bisani a miƙa wa Achike Udenwa, wanda ya mulki Imo daga 1999 zuwa 2007.

Tun wancan lokacin yake neman zama kujera lamba ɗaya a jihar. A zaɓen 2019, shi ne ɗan takarar gwamna karkashin inuwar Zenith Labour party.

Wani abokin mamacin na kusa-kusa ya ce ɗan siyasan ya mutu ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Jummu'a 24 ga watan Maris, 2023, kamar yadda Punch ta rahoto.

Bayanai sun nuna cewa mamacin ya riga ya biya miliyan N25m kuɗin Fam ɗin tsayawa takarar gwamna na jam'iyyar LP a zaben Imo da ke tafe ranar 11 ga watan Nuwamba.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN