Type Here to Get Search Results !

Mataimakin tsohon shugaban Najeriya Janar Abacha, Oladipo Diya ya rasu


Laftanar Janar Oladipo Diya, wanda ya yi mataimakin shugaban ƙasar Najeriya zamanin mulkin Janar Sani Abacha ya rasu. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

An taɓa yanke masa hukuncin kisa sakamakon yunƙurin juyin mulki amma kafin a zartar da hukuncin Abacha ya rasu.

Janar Oladipo Diya ya rasu ne a daren Lahadi a wani asibiti da ke Legas ya na da shekaru 78.

Babban É—an marigayin, Oyesinmilola Diya ne ya sanar da rasuwar.

An dai haifi Oladipo Diya ne a garin Odogbolu da ke Jihar Ogun a ranar 3 ga Afrilu, 1944.

A zamanin mulkin soja na Janar Muhammadu Buhari ya zama gwamann Jihar Ogun daga Janairun 1984 zuwa Agustan 1985.

Daga nan ya zama Babban Hafsan sojin Najeriya kafin likkafa ta yi gaba ya zama mataimakin shugaban ƙasa Janar Sani Abacha.

Sai dai Janar Abacha ya tuhumi Janar Diya da yunƙurin yi masa juyin mulki.

Kuma kotun soji ta tabbatar masa da laifin har ta yanke masa hukuncin kisa, amma kafin zartar da hukuncin Allah Ya yi wa Janar Abacha rasuwa.

Gwamnatin Janar Abdulsalami Abubakar kuma ta sake shi.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN