IGP ya tura jirgin sama da kayan damara don zaben jihar Kano


Gabanin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da za a yi ranar Asabar, babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, a ranar Juma’a ya aike da jirgin sama mai saukar ungulu na sa ido da sauran motocin aiki zuwa jihar Kano domin tabbatar da gudanar da atisayen ba tare da tangarda ba a jihar. Jaridar vanguard ta ruwaito.

 Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Mohammed Usaini Gumel wanda ya tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna ya fitar, ya kuma ce sun samu na’urorin yaki da tarzoma da kuma karin ma’aikata domin tabbatar da isasshen tsaro a yayin atisayen.

 Sai dai CP Gumel ya ce tare da karawa rundunar ta shirya tsaf domin an kammala shirye-shiryen tabbatar da gudanar da zabe cikin lumana a jihar.

 A cewar sanarwar, “Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sandan zaben gwamna da na majalisar jiha a shekarar 2023, CP Mohammed Usaini Gumel ta samu wani jirgin sama mai saukar ungulu na rundunar ‘yan sandan da ke sa ido, da karin ma’aikata, motocin aiki da kuma yaki da tarzoma.  

Kayayyakin da Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba ya tura jihar domin gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha a ranar 18 ga watan Maris 2023.

 Sanarwar ta kara da cewa "An shirya tsaf kuma an kammala shirye-shirye don tabbatar da gudanar da zaben cikin lumana."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN