Type Here to Get Search Results !

Main event

An ga watan Ramadan a Najeriya - Sarkin Musulmi


Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, a ranar Laraba ya ba da sanarwar ganin watan Ramadan a na shekarar 1444/2023.

Hakan dai na nufin za a fara azumin watan Ramadan ranar Alhamis a Najeriya. Jaridar Aminiya ta rahoto.

Sarkin Musulmin, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ya ce, “Yau Laraba, 29 ga watan Sha’aban, Hijira 1444, daidai da 22 ga watan Maris, 2023, an kawo karshen watan Sha’aban.

“Mun samu labarin ganin watan Ramadan daga shugabanni da kungiyoyin addinin musulunci a wurare da yawa a kasar nan, kuma kwamitocin ganin wata sun tantance sahihancin bayanan.

“Bisa ga haka, gobe Alhamis, 23 ga watan Maris ta zama daya ga watan Ramadan,” a cewar Sarkin Musulmi.

Ya yi kira ga al’ummar musulmi bayan kammala zaben 2023 da su dage da addu’a domin samun ci gaban kasa da Jihohi.

Ya kuma nemi masu kudi a cikin al’umma da su taimaki talakawa da gajiyayyu a lokacin ibadar azumin, musamman da abinci da sauran abubuwan bukata.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies