Ta Fara Karewa Kwankwaso, NNPP Ta Kori Dan Takara da Shugaban Jam'iyya a Jihar Arewa


Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari reshen jihar Katsina ta tsige ɗan takarar mataimakin gwamna, Muttaqa Rabe-Darma, shugaban jam'iya da sauran jagororin jiha
.

Jami'in hulɗa da jama'a na jam'iyyar NNPP, Nasiru Usman-Kankia, ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Jumu'a a Katsina, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce NNPP ta ɗauki wannan matakin ne saboda gano suna mata zagon ƙasa, ciki har da goyon bayan dan takarar gwamna a inuwar APC, Dakta Dikko Raɗda.

Usman Kankiya ya ce:

Kamar yadda kuka samu labari, wani bangaren shugabannin NNPP sun kira taro ba kan ƙa'ida ba ranar Alhamis 9 ga watan Maris, suka yanke shawarin da ya girgiza jam'iyya."
"A taron, wanda ɗan takarar gwamnan APC ya halarta, an gabatar da shugaban NNPP na jiha, Liti, ɗan takarar mataimakin gwamna, Rabe Darma da wasu kusoshi a matsayin masu sauya sheka zuwa APC."
"Ana bayyana haka, nan take wurin ya hargitse da hayaniya, aka fara jin tashin taken NNPP daga bakin magoya baya kuma suka riƙa nanata a'a, a'a, a'a."
Ya ƙara da cewa nan take ɗan takarar gwamnan APC ya yi karin haske cewa ya tattauna batun haɗa kai da NNPP, amma ba wai sauya sheƙa ba.

Kakakin NNPP ya tunatar da cewa tun a ranar 5 ga watan Maris, sun gargaɗi mambobi, shugabanni da 'yan takara su guji kulla kawance da kowace jam'iyar siyasa.

Su wa NNPP ta kora daga inuwarta a Katsina?
"Taron gaggawan da muka kira ya yi nazari kana ya yanke matakin korar duk wanda ke da hannu a taron cin amana, yayin da zamu saurari amincewar shugabanni na ƙasa," inji shi.

Ya ce waɗanda aka kora sun haɗa da, shugaban jam'iyya, Sani Liti, Sakataren jiha, Umar Jibril, shugaban matasa, Mustapha Basheer, shugaban shiyyar Katsina, Dauda Kurfi da takawaransa na Funtua, Abdullahi Mai'adua.

Sauran su ne shugaban jam'iyya na shiyyar Daura, Dakta Sale Mashi, ɗan takarar mataimakin gwamna, Rabe Darma, da kuma Sanata Audu Yandoma, kamar yadda PM News ta rahoto.

Nan da mako ɗaya tal, INEC zata gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya kuma Katsina na ɗaya daga wuraren da ake ganin sai APC ta yi dagaske.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN