Tashin Hankali Yayin Da Kwatsam Jigon Jam'iyyar PDP Ya Mutu A Hadarin Mota


Nasiru Nono, tsohon kakakin majalisar jihar Gombe, ya rasu a hadarin mota kan babban hanyar Abuja-Keffi, ranar Alhamis, 23 ga watan Maris. Legit ya wallafa.

Tsohon sakataren jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jihar Gombe, Buba Shanu, ya tabbatarwa The Punch rasuwar Nono, abin da ya ce labari ne mara dadi. Read 

A cewar Shanu, Nono yana tafiya ne tare da tsohon dan majalisar dokokin jihar, Hon Haruna Fada. 

Ya ce: "Shi (Nono), ya rasu a mummunan hadarin mota kan babban hanyar Abuja-Keffi. Yana tafiya ne tare da Hon. Usman Fada, tsohon dan majalisa wanda ya tsira kuma yana karbar magani." 

Nono ya yi fice cikin kakakin majalisun jiha a 2018 lokacin da aka ce wasu yan majalisa sun sace masa sandan iko. 

Amma, daga bisani yan sanda sun gano sanda a bayan harabar Kotun Ma'aikatu na Kasa a jihar, da aka tunanin wasu da ba a san ko su wanene ba suka yarda. 

Ya nemi zama sanata na Gombe ta Tsakiya a karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP a shekarar 2019 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN