Majalisar dokokin jihar Kogi ta dakatar da 'yan majalisar jiha guda 9 da kuma shugabannin kananan hukumomi Bakwai, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Ta ɗauki wannan matakin ne bayan kakakin majalisar, Honorabul Mathew Kolawole, ya karanta wasiƙar gwamna Yahaya Bello, wanda zargin 'yan majalisu 9 da hannu a aikata ta'addanci . Legit ya ruwaito.
Da yake faɗin ra'ayinsa kan zargin da ake wa mambobin guda 9, mataimakin shugaban majalisar, Alfa Rabiu Momoh, ya goyi bayan a dakatar da su nan take.
Ya ce jihar Kogi ta zarce duk wasu burikan son rai kuma ko kaɗan bai kamata a gano 'yan majalisa masu yin doka amma suna ƙarya doka da oda.
Haka zalika, Honorabul Collins Musa, mai wakiltar mazaɓar Omala, ya bi sahun matsayar mataimakin kakaki, ya ce duk batun da ya haɗa alaka da ta'addanci ya fi ƙarfin a rufe shi.
Bayan muhawara, majalisar ta amince ta dakatar da mambobin guda 9 har zuwa lokacin da aka kammala bincike kan zargin da ake masu.
Jerin mambobin da aka dakatar
Mambobin majalisar da matakin ya shafa sun ƙunshi, Olusola Kilani (Ijumu), Bello Hassan (Ajaokuta), Muhammed Lawi Ahmed (Okene 1), Moses Akande (Ogori Magongo), da Aderonke Aro (Yagba ta arewa).
Sauran su ne, Daniyan Ranyi (Bassa), Atule Igbunu (Ibaji), Atachaji Musa (Idah), da kuma Muktah Bajeh (Okehi)
Majalisa ta dakatar da wasu Coyamomi da mataimakansu
Bayan tattake wuri kan wancan batun, majalisar ta sake ɗaukar matakin dakatarwa kan shugabannin kananan hukumomi 7 kan zargin haddasa rikici a lokacin zaɓe.
Kananan hukumomin da aka dakatar da shuganninnsu da mataimaka sun haɗa da Bassa, Ogori/Magongo, Yagba ta yamma, Ibaji, Kabba/Bunu, Ajaokuta da kuma Adavi.
Leadership ta rahoto cewa majalisar ta kafa kwamitin mutum Bakwai karkashin jagorancin mataimakin kakaki, wanda zai gudanar da bincike kan ciyamomin guda 7.
Bugu da ƙari, majalisar ta dakatar da shugaban karamar hukumar Lokoja, Dansabe Muhammed, bisa zargin karkartar da wasu kuɗaɗe da suka kai miliyan N150m.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI