Dan sandan, wanda ke sanye da kayan sarki a lokacin, ya yi wannan aika-aika ne a bainar jama’a a wata makarantar firamare a safiyar ranar Alhamis a garin Ilori na Jihar Kwara. Jaridar Aminiya ta ruwaito.
Aminiya ta gano cewa dan sandan, yana aikin samar da tsaro ne a Gidan Gwamnatin Jihar Kwara, amma ya bi budurwar tasa makarantar inda ya harbe ta har lahira.
Wani ganau da ya nemi a boye sunansa ya ce sai da dan sandan ne ya fara zuwa makarantar firarame ta Redemption Model, inda bayan ’yan mintoci budurwar tasa ta kawo ’yarta makarantar.
Ganin ta ke da wuya, sai dan sanan mai mukamin Sajan ya dauko bindigarsa kirar AK-47, ya zo kusa da masoyiyar tasa ya harbe ta sau uku a kirji, nan take ta fadi a mace.
Daga nan sai dan sandan, wanda aka bayyana sunansa, Olalere Michael, ya juya bindigar ya dora ta a karkashin habarsa ya harbe kansa, shi ma ya ce ga garinku nan.
Mazauna unguwar sun ce kwankai kadan kafin kisan, dan sandan ya je gidan su budurwar tasa da ke unguwar Gaa Akanbi, inda ya kai mata hari da adda kan wani sabani da ke tsakaninsu.
Walinmu ya ziyarci gidan su mamacin, inda ya iske wata yayarsa cikin alhini, amma ta ce, “Ka yi hakuri, ba zan iya magana ba, don Allah.”
Mai magana na da yawun ’yan sanda na Jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, ya bayyana cewa abin da ya faru “rikicin tsakanin masoya ne, amma ba shi da alaka da zargin cin zali da ake wa ’yan sanda”.
Okasanmi ya ce, “Da muka samu labari, nan take Kwamishinan ’Yan Sanda, Paul Odama, ya tura jami’ai wurin aka dauke gawarwakin zuwa Asibitin Koyarw na Jami’ar Ilori, inda likitoci suka sanar cewa sun rasu
“Yanzu an fara bincike kan lamarin kuma da zarar an kammala za a bayyana wa jama’a sakamakon binciken”, in ji Okasanmi.
BY ISYAKU.COM