Muna jiranka a Kotu, APC ta mayar wa Obi martani kan zargin magudi a zaben shugaban kasa


Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce a shirye ta ke ta gana da Mista Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a gaban kotu kan ikirarin magudin zabe da ya yi a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

 Mista Bayo Onanuga, Daraktan Yada Labarai na Majalisar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na APC (PCC) ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja. Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.

 Bayanin hakan shi ne martanin jam’iyyar APC PCC kan kalaman Obi, a wani taron manema labarai a Abuja.

 “Muna maraba da matakin da Mista Obi ya dauka na neman hakkinsa a kotu idan ya gamsu da hujjojin magudin zabe da zai gabatar a gaban kotun kamar yadda yake zargi.

 Onanuga ya ce "Zuwa kotu wani bangare ne na tsarin zabe kuma shi ne matakin da ya fi dacewa. "

 Ya ce jam’iyyar APC PCC ta yaba da matakin, inda ya ce hakan shi ne dai dai marmakin a kira magoya bayansa su bazama kan tituna da tada zaune tsaye.

 Sai dai ya kalubalanci wasu takamammen ikirari a cikin jawabin da Obi ya yi wa manema labarai, yana mai cewa sabanin furucin nasa, ba gaskiya ba ne cewa zaben ba.a yi gaskiya da adalci ba.

 Onanuga ya ce zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na 2023 na daya daga cikin zabukan da aka gudanar cikin gaskiya da lumana a tarihin Najeriya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN