Ta faru: Gwamnatin jihar Kebbi ta hannun SSG Babale ta ki bada cikakken alkalumman yawan wadanda Yan bindiga suka kashe a Masarautar Zuru - Isyaku Garba ya yi zargi


Malam Isyaku Garba Zuru ya yi zargin cewa Gwamnatin jihar Kebbi ta hannun Sakataren Gwamnatin jihar ba ta da takamammen alkalumman kididdigan adadin yawan wadanda Yan bindiga suka kashe a Masarautar Zuru.

Ya yi zargin ne biyo bayan gazawar Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi SSG Babale Umar ya amsa wasu tambayoyi da Isyaku ya gabatar wa Gwamnatin jihar Kebbi ta ofishin Sakataren Gwamnatin.

Malam Isyaku Garba Zuru, ya bukaci sanin yawan adadin mutane da Yan bindiga suka kashe a kananan hukumomi hudu da ke Masarautar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi.

Isyaku ya yi amfani da dama da tsarin mulkin Najeriya ya ba kowane dan kasa karkashi sashe na 1 (1-3) na dokar damar samun bayani daga kowane hukuma ko ma'aikata Freedom Of Information Act 2011.

Ya bukaci sanin Mata, maza, yara nawa Yan bindigan suka kashe a kanan hukumomin Danko Wasagu, Fakai, Sakaba da Zuru daga 1 ga watan Janairu 2019 zuwa 31 ga watan Disamba 2022.

Adadin ya hada da shanu nawa Yan bindiga suka sace wa jama'a a wadannan kananan hukumomi, da kuma kiyasin gidaje nawa Yan bindiga suka kone tare da kayakin amfanin gona.

Kazalika takardar neman bayanin ta nemi sanin kiyasin adadin dukiyan bayin Allah da Yan bindiga suka halaka wa jama'a a wadannan kananan hukumomi.

Har ila yau, takardar ta bukaci bayani kan ko Gwamnatin jihar Kebbi ta saka tsoffin jami'an tsaro da suka kunshi Janar na siji da Mataimakan Safeto Janar na yan sanda ko sauran manyan jami'an tsaro masu murabus a harkar tsara dabarun tafiyar da harkar tsaro a Masarautar Zuru.

Daga karshe Malam Isyaku ya bukaci sanin ko Naira Miliyan nawa Gwamnatin jihar Kebbi ta kashe wajen gudanarwa tare da tafiyar da harkar tsaro a Masarautar Zuru daga 1 ga watan Janairu 2019 zuwa 30 ga watan Disamba 2022.

Ya kuma bukaci sanin adadin yawan jami'an tsaro da Yan bindiga suka kashe a tsawon lokacin da aka ambata da nassarori da Gwamnati ta samu .

Takardar ta farko ya aika wa Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi SSG Babale Umar ranar 9 ga watan Janairu 2023. Ya sake tunatar da shi a wata takarda ranar 6 ga watan Fabrairu. Ya kuma aike masa da takardar tunatarwa ta karshe kuma na uku ranar 6 ga watan Maris 2023 amma Babale ya yi biris ba bayani ko amsa kan lamarin a madadin Gwamnatin jihar Kebbi.

Kazalika Gwamnatin jihar Kebbi bata ce uffan ba dangane da wannan lamari. Yanayi da ya sa Malam Isyaku Garba Zuru ya yi zargin cewa Gwamnatin jihar Kebbi bata da cikakken alkalumman barna da Yan bindiga ke tafkawa al'ummar Masarautar Zuru amma tana kashe Miliyoyin kudi da sunan harkar tsaro.Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN