Jirgin yakin Amurka ya yi taho-mu-gama da na Rasha a sararin samaniya, duba yadda ta faru


Wani jirgin yaki mallakin kasar Rasha ya yi taho-mu-gama da jirgin Amurka mara matuki a sararin samaniya, saman tekun Black Sea. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

A cewar Rundunar Sojin Amurka a cikin wata sanarwar da yammacin Talata, lamarin dai ya tilasa mata saukar da jirgin nata cikin gaggawa.

Ta ce jirgin nata na kan shawagi ne a sararin samaniyar kasa da kasa, lokacin da jiragen yakin Rasha biyu suka yi yunkurin kakkabo shi.

Rundunar ta Amurka mai kula da kasashen Turai ta ce lamarin ya faru ne sakamakon gangancin Rasha.

Sai dai sanarwar ta ce Amurka za ta ci gaba da shawagin duk da barazanar.

“Jirginmu kirar MQ-9 na gabatar da shawaginsa a sararin samaniya lokacin da jiragen yakin Rasha suka yi yunkurin kai masa hari, lamarin da ya tilasta taho-mu-gama tare da kwace wa matukansa,” a cewar Shugaban Rundunar Sojin Saman Amurka, Janar James Hecker.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN