SIYASAR KEBBI: FADAKARWA A KAN KANFEN DA ZABE MAI ZUWA

FADAKARWA A KAN KANFEN DA ZABE MAI ZUWA                              


Sponsored post: Ya zama wajibi mu fadakar, don jan hankalin mutanen Jihar Kebbi sabo da mummunan hadarin da ke tunkaran mu sakamakon kanfe da zabe mai zuwa.

Babu shakka, ba'a taba kanfe na cin zarafi da tozartawa da wulakantar da juna tsakanin yan takara da kuma barazana ga ma'aikata da Sarakuna irin wannan.                                                     
Haka kuma, ba'a taba kanfe da a'ka kashe dukiya ba i'rin wannan. Hakika, babu daya daga cikin 'yan takara da ke da dukiyar da a'ke a'lmubazzanci da ita ba wai don neman zabe.      

Akwai kwakkwarar tuhuma cewa dukiyar da a'ake sayen jama'a, kudin bashi da ruwa ne. Kuma 'yan kwanakin nan an kashe makudan kudi da suka haura miliyan dari wajen sayen wasu jam'iyun da 'yan takarasu a garin Birnin-Kebbi kawai.            

Sanin kowane, dokar kasa ta hana amfani da kudi ko dukiya don neman zabe. Amma kash! Jami'an tsaro da Hukumar Zabe sun kasa yin komai a kan wannan mugun aiki. Ba wai a'kan i'don su a'ke aikata wannan ta'asa ba kawai, su ke bada cikakken tsaro a karya dokar kasa. A kwai hotuna da ke tabbatar da haka.              

Sanin kowa ne, shugabanci ba kasuwanci ba ne. Don haka, abin tambaya shi ne, ina wanda ya yi nasarar cin zabe zai biya bashin da ya karbo? Yaya wanda ya fadi zabe zai biya bashi?. Amsoshin wadannan tambayoyi karara su ke.

Wanda ya ci zabe zai yi  amfani da kudin mu ya biya kuma ya hannunta dukiyar mu da madafan ikon Jihar mu ga wanda ya bashi bashi sai yadda ya yi damu. Kuma mafi akasari, wadanda suka bada bashi da ruwa ba 'yan Jihar kebbi ba ne. Shi kuma wanda bai ci ba, zai jawo fitina don kowa ya rasa.

Sabo haka, muna cikin tsaka mai wuya muddin APC ko PDP dayan su ya ci zabe.        
Sabo da wadannan dalilai, muna kira da babbar murya ga dukkan 'yan a'salin Jihar Kebbi da mazaunan ta da mu guji zaben APC da PDP sabo da zaben kowannen su ba alheri ne ba gare mu da Jihar mu.                          

Biyan basussukkan da ake bin su, ba zai bada sukunin yima jama'a aiki da ci gaban al'umar mu ba. Kuma, mu na da kakkarfan zato na mai tayar da hankali muddin daya daga cikin su ya ci zabe.                   

Sabo da wadannan kwakwaran dalilai, muna kiran dukkan masu jefa kuri'a a fadin wannan Jiha da mu zabi duk dan takarar da mu kewa kyukyawan zaton gaskiya da a'dalci kan shi ko kan su. Mu rufawa kan mu a'siri Allah ya rufa mana.

Jam'iyar siyasa ba addini bace, kuma sai mun yi bayani a gaban Allah dalilin da yasa muka zabi duk wanda muka zaba. Ku sani babu wanda ke arzurtawa sai Allah. Allah ya yi muna jagora amin.                          

 MAWALLAFA

1. Alh. Amadu D. Jega
2. Alh. Shehu A. Argungu
3. Hajiya Rabi'atu Yabo Yauri
4. Aminu Z. Zuru

NB: Rubutu da aka wallafa a sama baya dauke da manufa, ko alhaki na shafin labarai na isyaku.com. Mawallafan rubutun su ne ke da alhakin abin da suka rubuta.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN