Ta faru: Mutumin da ya ba da maniyyinsa aka haifi yara sama da 500 zai fuskanci tuhumar kotu


An maka mutumin da ya yi sanadiyyar zuwa yara sama da 550 duniya a kotu bisa tsoron abin da ka iya biyo baya na auratayya tsakanin yaran, Telegraph ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa, Jonathan Jacob Meijer, wanda ke ba da maniyyinsa ga wadanda ba sa haihuwa a matsayin gudunmawa zai iya fuskantar fushin kotu. Legit ya wallafa.

Mutumin mai shekaru 41 na fuskantar kara ne da wata gidauniyar kasar Netherlands mai suna Donorkind Foundation, inda ta nemi a hana shi ci gaba da ba da maniyyinsa ga jama’a.

Hakazalika, gidauniyar ta zarge shi da shirga karya bisa bayyana adadin yaran da ya yi sanadiyyarsu zuwa duniya.

Yadda aka maka Mr. Meijer a kotu
Wata mata ‘yar asalin kasar Jamus ce ta shigar da karar, wacce aka ce ita ma ya ba ta gudunmawar maniyyin a 2018.

A ka’ida, mai ba da gudunmawar maniyyi zai bayar ne sau 25, ko kuma ya ba mata 12 don rage yaduwar auratayya tsakanin ahali daya da kuma matsalolin kwakwalwa ga ‘ya’yan da aka haifa, inji wani asibitin Jamus.

A cewar matar da ta shigar da karar:

“Idan da na san ya yi sanadiyyar zuwa yara sama da 100 duniya da ba zan zabe shi ba. Idan na tuna illar da hakan ke tattare dashi ga dana ba sai na ci ciwo a ciki na.”

Gidauniyar Donorkind Foundation tana neman kotu ta Mr Meijer ci gaba da ba da gudunmawa ga jama’a, sannan a binciko asibitin da yake kai gudunmawar.

Hakazalika, gidauniyar na neman a lalata dukkan maniyyin da Mr. Meijer ke dashi a ajiye a matsayin na gudunmawa, sai dai ga matan da a baya ya taba ba gudunmawar.

A halin da ake ciki, Mr Meijer na jerin bakin jadawalin masu ba da gudunmawar maniyyi ba bisa ka’ida ba a Jamus da ma sauran kasashen waje irinsu Denmark da Ukraine.

Hakazalika, gidauniyar ta bayyana cewa, mutumin yana ci gaba da bayyana halinsa na ba da gudunmawa a kafafen sada zumunta.

Wani rahoto ya ce, bincike ya ce direbobi masu tafiyar dogon zango ka iya fuskantar karancin maniyyi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN