Abun takaici: Yan bindiga sun kashe jaririn da aka haifa a wajensu, sun saki mahaifiyarsa a Kaduna


Wasu ’yan bindiga da suka yi garkuwa da wata mata mai juna biyu a Karamar Hukumar Kagarkon Jihar Kaduna sun sake ta bayan sun kashe jaririn da ta haifa a sansaninsu. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Rahotanni sun ce maharan sun saki matar ce mai suna Shamsiyya Mustapha, wacce aka sace tare da mijinta da kuma ’yarsu mai shekara 16 a kauyen Janjala da ke Karamar Hukumar ta Kagarko, ranar 5 ga watan Fabrairu.

Sai dai daga bisani maharan sun saki mijin matar bayan karbar kudin fansa Naira miliyan biyu da sabon babur da kayan abinci, amma suka ci gaba da rike matar da ’yar tasu har sai an kara musu wata miliyan biyun.

Da yake tabbatar da lamarin ta wayar salula ga wakilinmu, daya daga cikin ’yan uwan matar, Yakubu Datti, ya ce matar ta haifi jaririn ne a hannun ’yan bindigar ranar Lahadi.

Yakubu ya ce bayan sakin matar, ’yan bindigar sun kuma bukaci a ba su karin Naira miliyan daya da rabi kafin su saki ’yar tasu.

“Ka san lokacin da aka sace matar tare da mijinta da ’yar tasu, tana da juna-biyu na kusan wata bakwai. Sai ranar Lahadi da shugaban masu garkuwar ya kira dangin matar ya ce su zo su dauki ’yar uwarsu, ta haihu,” in ji shi.

Yakubu ya kuma ce ko da dangin suka nemi jin yadda za su yi su dauki jaririn, sai ’yan bindigar suka shaida musu cewa ai tuni sun riga sun kashe shi.

“Abin da kawai muka iya yi shi ne mun je mun dauko ta a wajen da shaida mana, kuma yanzu haka tana can tana samun kulawa a wani asibiti mai zaman kansa a Kagarko. Yanzu babban kalubalen shi ne yadda za a sake tara wata miliyan daya da rabin da za a kai a karbo ’yar matar da ke hannunsu.

Shi ma Madakin garin na Janjala, Sama’ila Babangida, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu ta wayar salula, inda ya ce yana cike da takaici a kan batun.

Ya ce yanzu haka yankin nasu ba shi da sakat saboida kusan kodayaushe ’yan bindigar na iya shiga da bindigu su dauki mutane yadda suke so.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ba ta magantu ba a kan lamarin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN