Biyo bayan wata mata ‘yar kasar Tanzaniya da ta yi alfahari da auren maza 3 a gida daya, wani lauya, Nicodemus Agweyo, ya bayyana cewa a daure ta a gidan yari.
Matar 'yar kasar Tanzaniya mai suna Nellie kwanan nan ta bayyana a kanun labarai a shafukan sada zumunta bayan ta bayyana cewa tana auren maza uku. Intelregion ta rahoto.
Wani abin da ya fi daure kai shi ne yadda aka bayyana cewa a cikin su ukun, daya daga cikinsu dan matar mahaifinta ne.
Ta ce, “Ni ce mai tasiri a kauye a wannan yanki don na auri maza uku. Na zauna da wadannan maza uku a matsayin mazana na tsawon shekara uku”.
Sanarwa ce da ta bar mutane da yawa cikin mamaki, wanda ya nuna gaskiyar cewa abin da ta aikata yana da hukunci da doka.
Lauyan na Tanzaniya ya bayyana cewa duk yadda doka ta amince da auren abokin zama fiye da daya, auren abokin zama fiye da daya laifi ne da doka ta hukunta.
Da yake zantawa da gidan talabijin na AYO TV, ya ce, "Idan mace ta auri fiye da mutum daya, za a yanke mata hukuncin zaman gidan yari na kasa da shekaru uku".
Lauyan ya kara da cewa wannan magana mai sauki ce domin babu zabin tara. Agweyo ya kara da cewa, mutumin da ya auri matar da ta riga ta yi aure, ko da addininsa ko al’adunsa sun yarda, shi ma yana da laifi kuma za a daure shi har zuwa shekaru uku a gidan yari.
Ku tuna cewa matar 'yar kasar Tanzaniya ta bayyana cewa auren maza fiye da daya ya faro ne ba da dadewa ba bayan mijinta na farko ya mutu a hatsarin mota kuma ya bar ta da 'ya'ya biyu.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI