Babbar Magana: Gwamnan APC Ya Samu Hujjojin Yadda Aka Yi Amfani da Sojoji Wajen Hana Shi Zarcewa


An ji Bello Matawalle yana kokawa cewa a maimakon ayi amfani da sojoji wajen kawo karshen rashin tsaro, sai aka yi amfani da su a harkar zabe.

Sojoji 50 a duk rumfar zabe

Gwamnan mai shirin barin-gado ya ce ta kai ana baza sojoji 50 a rumfar zabe saboda a shirya murdiya, kamar yadda ya fada, akwai hujjoji a bidiyo.

A cewar Gwamna Matawalle motoci fiye da 300 suka shiga jihar Zamfara a lokacin da ake shirin zabe, ya ce sojojin sun isa su gama da 'yan bindiga.

Kuma duk wata rumfa ta Zamfara ta zabe, babu wanda ke da soja kasa da 50 ga rumfunan zaben Zamfara.
Sannan kuma kai tsaye za ka ga cewa kiri-kiri idan ‘dan APC ka ke, ka ga soja yana bugunka cewa ba ka zabe.
- Muhammad Bello Matawalle

Matawalle zai je kotun zabe?

Da DW Hausa ta tambaye shi ko zai shigar da kara a kotu, Gwamnan ya nuna matakin ya rage ga jam’iyya, ya ce bai isa ya hana APC zuwa kotu ba.

Tun farko Mai girma Gwamna ya ce a matsayinsa na Musulmi yana mai godiya ga Allah SWT domin babu wanda ya yi tunanin zai samu mulki a 2019.

A zaben 2023, Lawal Dauda Dare da ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar PDP ne ya yi galaba a kan Bello Matawalle, ya hana shi zarcewa a kan mulki.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN