Yanzu Yanzu: Ƴan Shi'a Sun Dirar wa Abuja, Suna Nema A Bawa El-Zakzaky Fasfo ɗin sa


Da alama tsuguni bata ƙare ba ga mabiya Malam Ibrahim El-Zakzaky

Tun bayan da aka saki malamin, mabiyan sa suke ta gursheƙen faman ganin an bashi Fasfo din sa. Legit Hausa ya wallafa.

Wannan dalili yasa yanzu haka suka ƙara dira birnin tarayya Abuja, domin neman shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya cirewa El-Zakzaky dokar hana shi fita waje da aka saka masa.

Riƙe fasfon din bai tsaya akan Zakzaky ba, hattana matar sa, Malama Zeenah abin ya taɓa.

Fasfon ɗin dai idan an basu, suna iƙirarin zasuyi amfani dashi ne wajen fita ƙasar waje domin neman magani.

Abinda Gwamnatin Najeriya tace, taƙi wayon, domin kuwa ta gano dabarar su, saboda haka da sake.

A wani zama da tayi a Abuja, wata babbar kotu tuni ta shaida cewa buƙatar bawa Zakzaky da matar tasa Fasfo bazai samu ba.

Kotun ta umarci ƴan sandan farin kaya na Najeriya dasu cigaba da ajiye fasfon malamin da matar sa har sai lokacin daya kamata a bashi.

Da take zartar da hukuncin mai Shari'a Justice Obiora, ta yanke hukuncin cewa, Lauyoyin na Zakzaky sun kasa miƙa shaidu ƙwarara da zasu tabbatar da cewa, Fasfo ɗin sa ya ɓata.

Sun dira kotun, domin su nuna cewa hakika DSS ta ɗaukar masa Fasfo tun a shekarar 2018 lokacin daya dawo daga India kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN