Da Duminsa: DSS Ta 'Gano' Manyan Yan Siyasa Da Ke Shirin Kafa Gwamnatin Wucin Gadi Gabanin Mika Wa Tinubu Mulki


Hukumar yan sandan farin kaya, DSS, ta tabbatar cewa akwai wasu yan siyasa da ke da mugunyar nufi kafa gwamnatin wucin gadi a Najeriya, The Punch ta rahoto.

Shugaba Muhammadu Buhari zai mika mulki ne ga zababben shugaban kasa Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu. Legit ya wallafa.

Kakakin DSS ya tabbatar wasu yan siyasa na son kawo cikas ga mika mulki ga Tinubu
Amma, wasu yan siyasa suna ta kira ga shugaban kasa kada ya rantsar da Tinubu, inda suke cewa zaben da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ta APC ya ce ba amintaciyya bane.

A cikin wata sanarwa da ya fitar da ranar Laraba, 29 ga wayan Maris, mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya, ya ce yan sandan farin kayan sun tabbatar da yunkurin da wasu yan siyasa ke yi na hana Tinubu karbar mulki daga hannun Shugaba Buhari.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Hukumar yan sandan farin kaya, DSS, ta gano wasu manyan da ke shirya makarkashiya don kafa gwamnatin wucin gadi.

"Hukumar ta dauki wannan makircin, da wasu masu ra'ayin son kai shi shiryawa, a matsayin wani yunkuri na yi wa kundin tsarin mulki karan tsaye da doka saboda su jefa kasa cikin rikici da za a iya kauce wa.

"Ba za a amince da wannan haramcin ba a dimokradiyya da kuma ga yan Najeriya masu son zaman lafiya. Bugu da kari, hakan na faruwa ne bayan gudanar da zabe cikin lumana a mafi yawan sassan kasar."
DSS ta gargadi yan siyasa kan furta maganganu da ka iya tada zaune tsaye

A ranar Asabar, DSS ta gargadi yan siyasa su dena furta 'maganganun kiyayya' da 'karerraki' da ka iya tada rikici ko gwara mutanen kasa da gwamnati mai ci yanzu ta Muhammadu Buhari da mai jiran gado zababben shugaban kasa Bola Tinubu.

Wannan gargadin na DSS na zuwa ne bayan korafi da Karamin Ministan Ayyuka, Festus Keyamo ya yi na cewa DSS ta gayyaci dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi; da abokin takararsa, Datti Baba-Ahmed, kan kin amincewa da Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN