Kwana goma cif bayan Kotun Kolin ta yanke hukuncin a ci gaba da amfani da tsofaffi da sababbin takardun kudin na Naira 200 da 500 da N1,000, har zuwa karshen Disamban bana, kana Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele suka amince da hukuncin kotun, tun daga na wucin-gadi da kotun ta fara yi a ranar 8 ga watan Fabrairun da ya gabata zuwa hukuncin karshe na ranar 3 ga watan Maris din nan.
Da ma tun a watan Oktoban bara da Gwamnan Bankin CBN, ya ba da shelar cewa Gwamnatin Tarayya ta amince masa ya sauya fasalin takardun kudi na Naira 200 da 500 da 1,000, hantar wasu ’yan kasa ta fara kadawa, musamman wadanda suka saci kudin kasar nan, kasancewar sun san irin hasarar da irensu-irensu da talakawa suka tafka a 1984, lokacin da Shugaba Buhari yake matsayin Shugaban Kasa na soja.
Wasu daga cikin dalilan da Gwamnan Bankin CBN ya bayar na yin sauyin kudin a wannan lokaci sun hada da cewa, kashi 85 cikin 100 na kudin kasar nan suna boye a hannun mutane, inda kashi 15 cikin 100 ne kawai ke bankunan kasuwanci ana juyawa.
Wani hanzarin kuma shi ne, kokarin dakile ayyukan ’yan ta`adda da hana yin jabun kudi da ke yawaita.
Sabanin a wancan lokacin, inda Gwamnatin Buharin ta yi sauyin kudin bisa ga zargin ’yan siyasa da gwamnatinsa ta hambarar sun saci makudan kudi sun boye.
Bayan jin sanarwar Bankin CBN, sai aka ji Ministar Kudi da Kasafi da Tsare-Tsare, Hajiya Zainab Ahmed tana fada wa manema labarai a Abuja cewa, ma’aikatarta ba ta da masaniya a kan wannan niyya, saboda Gwamnan Bankin CBN bai tuntube ta ba, tana mai cewa lokacin bai dace ba kuma ba abin da sauyin zai haifar wa jama’a illa kara jefa su cikin wani mawuyacin halin tattalin arzikin da suke ciki.
Wasu masana tattalin arziki sun yi hasashe sabanin na Ministar, inda suka ce sauyin zai taimaka wa tattalin arzkin kasa.
A karshe dai Shugaba Buhari ya kawo karshen muhawarar dacewa da rashin dacewar sauya fasalin takardun kudin a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Tambarin Hausa.
A hirar, Shugaba Buhari ya kare sauya fasalin da wa’adin da aka diba na kwana 47, wato daga 15 ga Disamban bara zuwa 31 ga Janairun bana, inda ya ce za a iya canja su cikin wannan wa’adin muddin kudin na albashi ne ko na kasuwanci ba na haram ba.
Sau shurin masaki Shugaba Buhari ya sha fadin cewa gwamnatinsa ba za ta bari wasu su yi amfani da kudin jama’a don cim ma burinsu na cin zabe ba.
Sai ga shi yanzu rahotanni na tabbatar da cewa, an yi amfani da kudi da kayan masarufi wajen sayen kuri’a a zabubbuka biyu da aka yi, musamman na gwamnoni da majalisun dokoki na jihohi.
Fara sauya kudin ke da wuya sai matsalolin karancin sababbin takardun kudin ta zama ruwan dare, inda Bankin CBN ya ki samar da wadatattun takardun kudin da ya sauaya.
A takaice daga karshe, ta bayyana ga ’yan kasa cewa, Gwamnatin Tarayya da Bankin CBN bayan hana sayen kuri’a sun kuma shirya bullo da shirin takaita amfani da kudi a hannun jama’a da rana tsaka, ba tare da sanarwa ko wayar da kan ’yan kasa ba kamar yadda aka saba.
Da ma masu iya magana kan ce “Kudi kare magana” a dalilin sauya takardun kudin, ’yan kasar nan sun kara sanin ma’anar wannan karin magana, bisa yadda duk wata hada-hadar yau da kullum sai da ta kai ga wasu sun tsaya cik!
Kama daga saye da sayarwa a birane da karkara da tafiyetafiye na kusa da na nesa, kada ka yi batun bukukuwan aure da makamantansu, duk sai da suka faskara a kasar nan.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, wasu marasa lafiya sun mutu walau a kan an kai su assibiti an ce sai sun biya kudi ko su je su biya ta na’ura su kawo shaida kana za su samu kula, shaidar da ke wahalar bayyana a kan kari, saboda rashin sabis daga bankuna.
Akwai rahotannin da suka tabbatar da cewa, a wasu garuruwa da kasuwanni an yi cinikin ban-gishiri-in-ba-ka-manda saboda rashin tsabar kudi.
Bankunan sun kara tabarbara lamarin, kasancewar tun farko sun yi alkawarin cewa, za su rika barin mai ajiya ya dauki Naira dubu 500 a mako, sabanin Naira dubu 20 da suka kayyade kullum tun farko.
Kamfanoni da masu masana’antu za su iya daukar Naira miliyan 5 a mako, maimakon Naira dubu 100 a kullum.
Sai dai bankunan sun kasa cika wancan alkawari, al’amarin da ya kai ga bankunan suka rika rufe rassansu saboda ba su da tsabar kudin da za su ba wa abokan huldarsu.
Rashin kudin da jama’a suke ciki da rashin man fetur, sun sa dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC kuma zababben Shugaban Kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya fito karara ya yi zargin cewa zagon kasa ake yi masa.
Sai dai Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin.
Wasu daga cikin gwamnonin APC irin su Dokta Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano da Malam Nasiru El-Rufa’i na Jihar Kaduna fitowa karara suka yi, suka soki lamirin Gwamnatin Tarayya da Gwamnan Bankin CBN kan halin da ’yan kasa suka shiga na rashin kudin.
Malam Nasiru ma cewa ya yi, makusantan Shugaba Bahari (Kabal) da suka kasa tsai da dan takararsu na neman shugabancin kasa ne kanwa uwar gamin wannan lamari saboda ba sa son Tinubu ya kai labari.
Jam’iyyar APC ta kasa da ofishin Shugaban Kasa sun musanta wannan zargin.
Duk wanda ya isa a kasar nan sai da ya yi kira ga Shugaba Buhari da Gwamnan CBN su kawo karshen wannan masifa ta hanyar bin umarnin hukuncin Kotun Koli, amma suka yi biris!
Har zanga-zanga jama’a suka rika yi a wasu jihohin Kudu, zanga-zangar da ta haddasa asarar rayuka, ba ya ga wadanda suka jikkata, amma ina!
Har sabon Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) sai da ya ba wa Gwamnatin Tarayya wa’adin mako daya ta bi umarnin Kotun Koli da kawo karshen karancin man fetur, wa’adin da yake karewa a wannan makon.
Wasu na da ra’ayin cewa, kamata ya yi Shugaba Buhari ya yi amfani da ikonsa wajen sa jami’an tsaro su gano masa duk inda wadanda suka saci kudaden da yake zargi suke tare da kwace su.
Wadanda za a iya gurfanar da su a gaban shari’a a gurfanar da su, wadanda kuma suke da rigar kariya a jingine kai su kotu sai sun sauka daga mulki.
Amma maimakon hakan sai ya yi wa ‘yan Najeriya fyadar ’ya’yan kadanya, lamarin da ya kara jefa ’yan kasa cikin karin mawuyacin kuncin rayuwa.
Allah Kada Ka maimaita mana irin wannan sauyi!
Rahotun Jaridar Aminiya
BY ISYAKU.COM