Inna lillahi: Mutane 35 sun mutu a hatsarin mota guda 2 a Kebbi – FRSC


Mutane 35 ne suka mutu a wasu hadarurruka guda biyu da suka faru a Kebbi ranar Lahadi da kuma Litinin.

 Kwamandan hukumar FRSC reshen jihar, Mista Yusuf Aliyu-Haruna, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Binrin Kebbi ranar Talata cewa wasu mutane 40 sun samu raunuka daban-daban a hadarin.

 Ya kara da cewa hadarin ya rutsa da motoci uku ne.

 “Mutane 12 ne suka rasa rayukansu a hatsarin da ya afku a kan hanyar Kalgo zuwa Bunza a ranar Lahadin da ta gabata wanda ya hada da motoci biyu.

 “A ranar Litinin, mutane 23 ne suka rasa rayukansu yayin da suke tafiya cikin wata babbar mota dauke da hatsi iri-iri daga Illela zuwa Ibadan a kan hanyar Jega-Koko.

 “An kai wadanda suka jikkata zuwa manyan asibitoci a kananan hukumomin Kalgo da Jega,” inji shi.

 Aliyu-Haruna ya danganta faruwar hadurran da yawan lodi, saurin gudu da kuma amfani da tayoyin da wa'adin ingancinsu ya kare.

 Ya kuma gargadi masu ababen hawa, musamman direbobin motocin ‘yan kasuwa da su guji wuce gona da iri da kuma amfani da tayoyin da ingancinsu ya kare domin tabbatar da tsaro a kan manyan hanyoyin.

 Kwamandan sashin ya shawarci masu ababen hawa a kan shan abubuwan da ba a sani ba, sannan ya bukaci fasinjoji da su goyi bayan fafutukar yaki da tukin ganganci a Kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN