Hukumar NDLEA ta gurfanar da wasu ’yan uwa mata biyu da mijin daya daga cikinsu a gaban manema labarai a Katsina ranar Talata bisa samunsu da laifin mallakan kilo shida na yanar wiwi. NAN ya ruwaito.
Kwamandan hukumar a jihar Katsina, Mista Mohammed Bashir, ya shaidawa manema labarai cewa an kama daya daga cikin matan Rabi Musa mai shekaru 45 da laifin mallakan kilo uku na tabar wiwi.
Ya ce Rabi tana taimaka wa mijin nata, wanda a halin yanzu yake sayar da haramtattun kwayoyi tare da ‘yar uwarta, Zainab Musa da mijinta.
Ya ce an kuma kama Zainab da mijinta da laifin mallakar wani karin kilo uku na tabar wiwi.
Bashir ya ce kama Rabi ya kai ga cafke sauran mutane biyun da ake zargin, ya kuma ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a kama mijin nata da ya gudu.
Mutum ukun da tuni aka kama za a gurfanar da su gaban kuliya, in ji shi.
Ya kuma dora laifin yawaitar kashe aure a jihar Katsina kan shaye-shayen miyagun kwayoyi, ya kuma yi kira ga iyaye da su dinga zuwa a yi gwajin da zai nuna diyansu basu tu'ammali da kwayoyi kafin a daura aure. .
Ya kuma bayar da shawarar cewa dole ne iyaye su bukaci surukai da nemi satifiket na tabbacin rashin shan miyagun kwayoyi kafin su aurar da ‘ya’yansu mata maimakon a rude su da dukiya.
Da take amsa tambayoyi daga manema labarai, Rabi mai shekaru 45 da haihuwa ta amsa laifin aikata laifin amma ta bayyana cewa tana aiwatar da umarnin mijinta ne kawai domin a gan ta a matsayin mace mai aminci da biyayya ga miji.
Ta roki a yi mata afuwa sannan ta shawarci mata da iyaye da su yi taka tsantsan wajen neman auren ‘ya’yansu mata.
BY ISYAKU.COM