An fara: Buhari ya ce yana son Tinubu ya ci gaba da yiwa 'yan kasa abu 1 da yake yi


Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana cewa, ya yi shimfidin yaki da rashawa mai dorewa a gwamnatinsa na shekara takwas mai karewa. Legit ya wallafa.

Shugaban ya kuma bayyana cewa, yana fatan gwamnati mai jiran gado za ta bi tafarkinsa na tabbatar da ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, Channels Tv ta ruwaito.

Shugaban ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis a lokacin da ya gana da mahukuntan kotun da’ar ma’aikata karkashin jagorancin shugabanta Danladi Umar a gidan gwamnati da ke Abuja.

Ya bayyana cewa, rashawa babbar illa ce ga kowace kasa a duniya, inda ya yaba da kokarin da kotun yake yi wajen yakar rashawa.

Hakazalika, ya kuma yabawa shugaban tawagar da ta gana dashi da kuma sauran hukumomin yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Ya ce, sun tsaya tsayin daka don tabbatar da an fatattaki rashawa a Najeriya duk da kuwa babu wadatattun ma’aikata da kudaden gudanar da ayyukan, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake magana, Buhari ya ce:

“Fatanmu ne a ce tubalin da muka kafa a gwamnatin nan zai ci gaba da tafiya, kasancewar batun rashawa lamari ne da ke zama babbar barazana ga dukkan kasashe.”
Kafin hawansa mulki a Najeriya, daya daga cikin abubuwan da Buhari ya yiwa ‘yan Najeria alkawari akwai tabbatar da yaki da rashawa a kasar.

Sai dai, a baya kun ji yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da yiwa tsoffin gwamnonin jihohin Taraba da Filato bayan da aka tabbatar da sun ci kudin kasa kuma an daure su a kotu.

Wannan lamarin ya haifar da cece-kuce a Najeriya, amma duk da haka aka sake su tare da wanke su daga laifin bisa umarnin manyan masu fada a ji a Najeriya.

Daya daga abin da ke ba gwamnatin Najeriya shine tabbatar da hukuncin kotu kan ayyukan rashawa da aka gudanar a kasar nan, musamman kan manyan ‘yan siyasa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN