Madalla: Daruruwa 'yan Boko Haram sun yi saranda, sun mika wuya ga soji a Borno, duba dalili


Daruruwan ‘yan Boko Haram ne suka mika wuya tare da ajiye makamai a cikin kwanaki hudu bayan da suka samu sabani da kazamin fada a tsakaninsu. Legit ya ruwaito
.

Hakazalika, ragargazar da rundunar sojin sama da na kasa na Najeriya suka yi sa daruruwan ‘yan ta’addan sun tsere daga sansaninsu da ke Gaizuwa a Bama da ke jihar Borno.

A cewar rahoto, ‘yan ta’addan 119 ne tare da iyalansu suka mika wuya tare da ajiye makamai ga jami’an rundunar Operation Hadin Kai.

Wasu kuwa sun mika wuya a Konduga, yayin wasu suka tsere ta yankin Dikwa da ke bullewa suka tafkin Chadi, kafar Labarai ta Zagazola Makama ta tattaro.

Hakazalika, da yawan ‘yan ta’addan sun mika wuya tare da ajiye makamai da kayan fashewa ga jami’an tsaro a kusa Gueskerou a Diffa da ke jamhuriyar Nijar.

Duba da yadda abubuwa ke tafiya, ‘yan ta’addan Boko Haram sun amsa ‘yan ta’addan ISWAP sun fi karfin su a yankunan da kungiyoyi biyun ke aikata ta’addancinsu.

Ana ci gaba da samun nasara kan ‘yan ta’addan a bangarori daban-daban na Najeriya, kamar yadda rahotanni da alkaluma ke nunawa.

A wani labarin kuma, kun ji yadda ‘yan ta’addan Boko Haram suka farmaki al’ummar Goza a jihar Borno ba a ranar Asabar, ranar da aka yi zaben shugaban kasa a Najeriya.

Sarkin Goza, Mohammed Shehu Timta ya tabbatarwa majiya wannan lamari, inda ya ce an farmaki mutanen garinsa ne a lokacin da suke kokarin kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar.

Ya ce:

"Kungiyar Boko Haram ta kawo mana hari har cikin kwaryar gari, suka bude wuta kan mai uwa da wabi, mutane 5 suka ji raunuka kuma tuni aka garzaya da su Asibiti a Maiduguri domin kula da lafiyarsu." 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN