Miye laifinsu: Gwamnan PDP ya kori dukkan masu mukaman siyasa a jiharsa bayan ya sha kaye a zabe


Gwamnan Jihar Abia da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya, Okezie Ikpeazu ya amince da korar dukkan masu mukaman siyasa a jihar, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Sakataren gwamnatin jihar Anambra, Barrister Chris Ezem ne ya fitar da sanarwar korar masu mukaman siyasan.

Rukunin wadanda Gwamna Ikpeazu ya sallama daga aiki

Wadanda abin ya shafa sun hada da: Mataimaka na musamman, Manyan mataimaka na musamman, Mashawarta na musamman da jami'ai na fasaha.

Wannan kari ne bisa masu mukaman siyasa da gwamnan ya kora bayan ya gaza yin nasarar cin zabe don zuwa majalisar dattawa kuma wanda ya so ya gaje shi ya sha kaye a zaben gwamna.

Ikpeazu ya umurci Akanta Janar ya biya wadanda aka kora albashin Maris
Gwamnan ya kuma umurci Akanta Janar na jihar ya tabbatar an biya albashin watan Maris ga dukkan masu mukaman siyasan da aka kora nan take.

Gwamnan ya musu godiya bisa gudunmawar da suka bada da ayyukansu ga jihar sannan ya musu fatan alheri a ayyukan da za su yi a gaba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN